26 Mayu 2026 - 10:56
Source: ABNA24
Kudancin Lebanon; Yankin Da Ke Alamta Nasarar Al'umma Da Rashin Nasarar Isra'ila 

Kudancin Lebanon ya sami 'yanci albarkacin jaruman gwagwarmaya da 'ya'yan wannan ƙasa, a irin wannan rana shekaru 26 da suka gabata   kuma mamaya bayan shekaru da yawa dole su ka bar wannan yanki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait (AS) - ABNA -: A cikin shekarun ƙarshe na karni na ashirin, mamayar kudancin Lebanon da sahayoniyar ta yi, wadda ta fara tun 1982, ta zama ɗaya daga cikin mamayar soji mafi tsayi a tarihin zamani. Wannan mamaya ta kasance cikin tsadar rayuka da kuɗi ga mamaya.

Ci gaban gwagwarmayar sojojin Lebanon, musamman Hizbullah, wadda ta hanyar hare-haren kwanton bauna da kai hari daidai kan wuraren mamaya, ta sanya asarar mamaya ta zama mai wuya ga sahayoniya, daga ƙarshe ta haifar da janyewar bai-daya na sojojin sahayoniya a ranar 24 ga Mayu, 2000.

Wannan janyewar ta faru ne ba tare da cimma burin da aka ayyana ba, kuma ƙarƙashin matsin lamba na ra'ayin jama'a a cikin Isra'ila da kuma asarar rayuka masu yawa, wanda an rubuta shi a matsayin wani muhimmin sauyi a tarihin gwagwarmayar Lebanon. Gwamnatin Lebanon ta sanya wannan rana a matsayin "Ranar gwagwarmaya da 'Yanci", wanda ya zama alamar nasarar azamar al'umma a kan mamaya. Tun daga wancan lokacin, fiye da shekaru 25 da suka shude, amma sahayoniya ba ta taɓa samun kwanciyar hankali a iyakokinta na arewa ba. Rahotanni da yawa sun nuna cewa sahayoniyoyi tare da keta sararin samaniyar ƙasar Lebanon akai-akai, suna ci gaba da ayyukan leƙen asiri, kai hare-hare a wurare, har ma da kisan gilla.

Wannan tsarin na ta'addanci ya mayar da kudancin Lebanon ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake fama da rikici a yankin, kuma ya sa sahayoniya ta zama babbar tushen rashin kwanciyar hankali da haifar da rikici a Gabas ta Tsakiya. Cin zarafi da keta iyaka na ci gaba, ciki har da hare-haren sama da ta ke kaiwa ƙauyuka da garuruwan da ke kan iyaka, wannan hare-hare basu raunanata gwagwarmaya ba, kai sai dai ma ya zama abin ƙarfafa ƙarfin aikin soja na Hizbullah. Hizbullah ta Lebanon a cikin waɗannan shekaru, ta dogara da kwarewar fage, goyon bayan jama'a, da ƙirƙirar sabon tsaro, ta sami damar ƙirƙirar hadaddiyar cibiyar tsaro. Ayyukan nasara na jirage marasa matuka, rokoki, da makamai masu linzami a matsayin martani ga cin zarafi da keta iyaka, suna nuna girma na inganci da yawan ƙarfin wannan rundunar gwagwarmayar. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ƙaruwar farin jini da halaltacciyar Hizbullah a tsakanin mabambantan kungiyoyin al'ummar Lebanon ta samu.

Mutanen Lebanon suna kallon Hizbullah ba kawai a matsayin ƙungiyar siyasa ta soja ba, sai dai a matsayin mai kare ƙasa daga maƙiyi na waje. Wannan farin jini ya samo asali ne daga nasarar da gwagwarmaya ta samu a 'yancin kai na shekara ta 2000 da kuma kare Lebanon daga hare-hare makiya, wanda ya haifar da ƙarin haɗin kan ƙasa. 'Yancin kudancin Lebanon a shekara ta 2000 yana da fannoni da yawa. Ta fuskar soja, wannan lamari ya nuna cewa mamayar soji na wasu ƙasashe tare da biyan farashi da bai dace ba, a ƙarshe yana haifar da rashin nasara. Sahayoniya da a baya take da'awar cewa tana da cikakken ƙarfin soji, ta fuskanci rashin nasara akanta, sai gas hi sojojinta a kudancin Lebanon ma sun durkushe.

Emile Lahoud, tsohon shugaban Lebanon, a yau (Litinin) yayin da yake yaba wa nasarorin mayakan gwagwarmayar Lebanon a kan mamaya a fagen kudancin Lebanon, ya ce: "Bikin gwagwarmaya da 'yanci a wannan shekara yana gudana ne a wani lokaci na tarihi, musamman ma cewa maƙiyin da muka sami 'yanci daga gare shi a shekara ta 2000, yana neman sake mamaye kudu, amma ya fuskanci gwagwarmayar jaruman juriya".

Lahoud ya kara da cewa: "Wannan halin da muke ciki ya sa mu a wannan rana mu tuna da waɗanda suka sami nasara da 'yanci, domin abin da zai faru nan gaba kadan, zai yi kama da abin da ya faru a shekara ta 2000, kuma maƙiyi, duk da laifukansa, bai iya tilasta abin da yake so ba a Lebanon ko a yankin".

Joseph Aoun, shugaban Lebanon na yanzu, a ranar tunawa da 'yancin kudancin Lebanon, ya nanata cewa "ficewar sahayoniya gaba ɗaya daga ƙasar, zai kasance buƙatar ƙasa mai tsayi, kuma ba za mu yi kasala ba; Lebanon ba za ta karɓi ci gaba da cin zarafi da mamaya ba".

Ya nanata: "A shekara ta 2000, sakamakon gwagwarmayar 'ya'yan wannan ƙasa da sadaukarwarsu, mamaya sun ja da baya, kuma ranar 25 ga Mayu ta kasance ranar girmamawa ta ƙasa baki ɗaya".

Kafin wannan kuma, Sheikh "Naim Qassem", sakatare janar na Hizbullah ta Lebanon, a munasabar ranar tunawa da bikin gwagwarmaya da 'yancin kudancin Lebanon daga mamayar sahayoniya, ya yi jawabi game da batutuwa daban-daban ciki har da yanayin siyasar Lebanon, Iran, Bahrain, da Falasdinu.

Ya ce: "Duk wanda ya taimaka wagwagwarmaya, shi ne abokin tarayya a gwagwarmaya da 'yanci. Gwagwarmaya tare da sojoji da jama'a, tuaku uku ne wanda ya sami damar cimma nasarar 'yanci. Nasarar 'yanci (kudancin Lebanon) sakamakon haɗin gwiwar gwagwarmaya, sojoji, da al'ummar Lebanon ne. Wannan muhimmin abu ne kuma mai tasiri a cimma 'yanci. Bikin gwagwarmaya da 'yanci biki ne na dukan Lebanoniyawa da 'yanci a duniya, kuma biki ne na Falasdinu.

Sakatare janar na Hizbullah ya nanata: "Ya kamata mu tuna a cikin zukatanmu cewa, bugun gwagwarmaya a shekara ta 2000 ya tilasta wa mamaya ficewa daga yankin iyaka.

Ta fuskar siyasa, wannan nasarar ta taimaka wajen ƙarfafa gwagwarmaya a yankin, kuma ta zama abin koyi ga sauran ƙungiyoyin neman 'yanci. Ta fuskar yan'adamntaka, komawar dubban 'yan Lebanon da suka rasa muhallansu zuwa gidajensu da kuma ƙarshen wahalar mamaya, alama ce ta fata da juriya. A cikin shekaru bayan 2000, sahayoniya ta bi manufar haifar da tashin hankali tare da fakewa daaa batutuwa kamar "barazanar Hizbullah" ko takaddama kan iyaka kamar gonakin Sheba'a. Wannan manufar a lokuta daban-daban, ciki har da yaƙin kwanaki 33 na shekara ta 2006, ya haifar da asara mai yawa ga ɓangarorin biyu, amma a ƙarshe ya ƙara ƙarfafa gwagwarmayar Lebanon. Hizbullah ba wai kawai ta fita daga waɗannan jarabawowi cikin nasara ba ne sai dai ma tare da haɓaka makamai da sabbin dabaru, ta zama mai hana ke ta iyaka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha